1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin yan adwar Jamus ga aiki a Afganistan

Halimatu AbbasDecember 27, 2010

Babbar jam'iyyar adawa a Jamus ta nuna rashin amincewa da tura dakarun kasar zuwa Afganistan.

https://p.dw.com/p/zq8e
Frank-Walter SteinmeierHoto: AP

Shugaban babban jam'iyyar adawar Jamus ta Social Democrats, Frank Walter Steinmeier ya ce jam'iyyarsa ba za ta goyi bayan tayin da ƙasar tayi na aikawa da dakarun sojojin ƙasar zuwa Afghanistan ba sai an ɗauki matakan da suka nuna cewa Jamus za ta fara rage aikawa da dakarunta zuwa ƙasar. A wani hira da yayi da jaridar "der Bild" na ranar Lahadi a nan Jamus, Steinmeier ya ce dole a amabci lokacin da Jamus zata fara janye dakarunta daga ƙasar ta Afganistan kafin ta ba da na ta goyon bayan. A yanzu haka dai Jamus na da kimanin dakaru 4800 a Afganistan kuma al'ummar ƙasar da dama na adawa da wannan lamarin.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Halima Balaraba Abbas